Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Matakin nadin da akayi wa attajirin Aziz Akhannouch, na zuwa ne bayan da gungun jam'iyyun adawa na kasar suka yi rinjaye a zaben ‘yan majalisun dokokin kasar.
A Marocco dai shi ne karon farko da jam'iyyar PJD ta masu matsakaicin kishin addini da ke mulkin kasar, ta sha mummunan kaye a zaben 'yan majalisun dokoki.
Gungun jam'iyyun 'yan adawa ne dai suka kawo karshen rinjayen da jam'iyyar take da shi.
342/